20 Afirilu 2021 - 14:53
A Yau Ne Za A Fara Yi Wa Mutane Miliyan Daya Allurar Rigakafin “Corona” A Iran

Ministan kiwon lafiya na Iran Sa’id Namaky ya bayyana cewa bayan jinkirin da aka samu na wasu makwanni, daga yau za a fara yi wa mutane allurar rigakafin ta cutar corona.

ABNA24 : Ministan kiwon lafiyar na Iran ya kara da cewa;allurar rigakafin da za a fara daga yau zuwa nan da mako guda, za a yi mutane miliyan daya.

Dr. Namaki ya kuma bayyana cewa a matakin farko wadanda za a yi wa allurar rigakafin sun hada ma’aikatan kiwon lafiya a fadin kasar da kuma masu dauke da cutuka masu hatsari,kamar masu fama da ciwon daji, da kuma cutuka masu karya garkuwar jiki.

Har ila yau, ministan na kiwon lafiya ya bayyana fatansa na ganin cewa an da zarar an gama da mataki na farko na wadanda za a yi wa rigakafin, a shiga zagaye na biyu.

342/